BUHARI 12 A WATANNI 12 RAHOTON MUSAMMAN: Nasarorin Shugaba Buhari 12 A Watanni 12

Go down

BUHARI 12 A WATANNI 12 RAHOTON MUSAMMAN: Nasarorin Shugaba Buhari 12 A Watanni 12

Post by Admin on Mon Jun 06, 2016 6:30 am

Yayin da gwamnatin Shugaba
Muhammadu Buhari ke shirin cika
shekara daya, shin ko da hawansa
mulki abubuwa sun ci gaba da
kasancewa kamar yadda suke a baya?
babu shakka amsar ita ce, a’a. Daga ranar 29 ga watan Mayun 2015,
ranar da aka rantsar da Shugaba Buhari
zuwa yanzu, ko shakka babu abubuwa
sun canja kwarai da gaske. A lokacin da
yake yakin neman zabe daga watan
Janairun 2015 zuwa watan Maris, Shugaba Buhari ya yi wa ‘yan Nijeriya
alkawarin cewa, idan Allah (S.W.T) Ya ba
shi nasara, zai fi maida hankali a kan
abubuwa uku, su ne; tsaro, kawar da cin
hanci da rashawa da kuma bunkasa
tallalin arziki, kan hakan idan aka ce Shugaba Buhari ya samu nasara fiye da
kaso 80 cikin 100, ba a yi kuskure ba,
ganin yadda gwamnatinsa ta samu
gagarumar nasara a wadannan
bangarori. Idan mai karatu na biye da ni,
ina nan zane da nasarori 12 a watanni 12 kamar haka: 1. Tsaro; lallai tsaro shi ne lamba daya a cikin skowace al’umma a duniya, lokacin
da shugaba Buhari ya karbi ragamar
jagorancin Nijeriya, tsaron kasar na
kokarin kubucewa ne daga hannun
mahukunta, domin kuwa wani sashe na
Nijeriya da ya kai girman kasar Belgium baki daya na hannun ‘yan ta’addan
Boko Haram, a wancan lokaci dukkan
kananan hukumomi 14 na jihar Borno
da guda 3 daga jihar Adamawa, na
karkashin ikon Boko Haram, su ke da
iko da kananan hukumomin, hasali ma sun cire tutocin Nijeriya tare da maye
gurbi da tutocinsu. Kazalika suka canja
sunayen kananan hukumomin, cikin
watanni 12 hakan ya zama tarihi,
dukkan wadannan kananan hukumomi
sun dawo karkashin ikon Nijeriya, dubban mutanen da suka yi gudun
hijira daga jihohin a yanzu sun koma
muhallinsu, zaman lafiya ya dawo,
gidajen da ‘yan Boko Haram suka
rurrushe yanzu ana sake gigginawa,
kasuwannin garuruwan duka an bude su, rayuwa ta koma kamar yadda take a
baya. 2. Kubutar da mutane sama da 12,000 daga hannun Boko Haram, kafin zuwan
Shugaba Buhari, bayan kubucewar
tsaro a kusan gaba dayan yankin Arewa
Maso Gabas, dubban mutane, manya,
yara, maza da mata sun shiga hannun
‘yan Boko Haram a matsayin bayi, amma a ranar da ya karbi ragamar mulki,
Shugaba Buhari ya fara canja fasalin
tsaro, ya bada umarnin mayar da manya
madafun iko na rundunar sojojin kasar
nan zuwa Maiduguri, wannan ya
taimaka wajen tabbatar da dawowar tsaro a yankin, sakamakon haka
rundunar jami’an tsaron Nijeriya sun
kubutar da mutanen da Boko Haram
suka sace ta karfi da yaji fiye da dubu 12
a cikin watanni 12. Bayan kubutar da
dubban mutanen, gwamnatin Muhammadu Buhari a yanzu ta maida
hankali wajen ganin sun koma
rayuwarsu cikin walwala fiye da yadda
suke yi a baya. 3. Matatun man fetur; kafin zuwan Shugaba Buhari matatun man da muke
da su a kasar nan, da suka hada da;
Matatar Port Harcourt, jihar Ribers, Warri, Jihar Delta da kuma ta jihar Kaduna,
dukkanin su ba wadda take ba da mai
koda kuwa lita daya, kuma sun kasance a hakan shekara da shekaru, daga
zuwan gwamnatin Buhari, matatun
duka sun dawo aiki cikin kankanin
lokaci duk da yawan masu yi musu
zagon kasa, a yanzu haka dukkan su na
aiki, suna kuma tace mai fiye da lita milyan 7 a rana, sai dai kash, makiyan
Nijeriya da ci gabanta sun kassara
aiyukan matatun ta hanyar farfasa
hanyoyin da suke kai danyen man daga
inda ake hakowa zuwa inda ake tacewa.
Koda yake tuni gwamnatin Shugaba Buhari ta ba da umarnin bin duk hanyar
da suka dace wajen gyarawa tare da
kare faruwar hakan a nan gaba. Cikin
watanni 12, gwamnatin Buhari ta yi
abun da gwamnatocin baya suka kasa
yi a shekaru fiye da 12. 4. Tallafawa jihohi da kudaden biyan ma’aikata albashi; a lokacin da Shugaba
Buhari ya karbi ragamar mulkin kasar
nan, fiye da rabin jihohin kasar ba sa iya
biyan ma’aikatansu albashi, hakan ya yi
matukar tayarwa Shugaba Buhari
hankali kasancewarsa shugaban talakawa, ya kuma san yadda hakan zai
haifar da kunci da rashin walwala a
zukatan ma’aikatan musamman kanana,
wannan ya sa a watan Satumbar da ya
gaba, ya bada umarnin fitar da naira
bilyan 689.5 da babban bankin kasa na CBN, don rabawa jihohi 27, a matsayin
tallafi don su samu damar biyan
ma’aikata hakkokinsu. 5. Kakkabe ma’aikatan bogi; kafin zuwan gwamnatin Shugaba Buhari, a
kowane wata, gwamnati na asarar naira
bilyan 2.2 wajen biyan ma’aikatan bogi
su fiye 34,000 da wasu ‘yan tsirarun
mutane suka rubuta na karya suna
amshe kudaden a duk karshen wata, zuwan Shugaba Buhari ba dadewa
bayan gudanar da bincike aka gano
hakan. A cewar Ministar Kudi, Madam
Kemi Adeosun, binciken farko an gano
ma’aikatan bogin kimanin 23,000, daga
baya aka sake gano 11,000, wadannan dukkan su a rubuce ne amma babu
ma’aikatan a zahirance. Gwamnatin
Shugaba Buhari ciki watanni 12 ta yi
wannan namijin kokari 6. Asusun bai daya na TSA; Shugaba Buhari ya zo ya tarar da asusun ajiya na
gwamnatin tarayya fiye da 1000,
wadanda da damansu an bubbude su
ne ba bisa ka’ida ba, kuma zai yi
matukar wahala a gane wadanne ne
sahihai, wadanne ne na bogi, don haka ya bada umarnin duk wata hukuma da
ke karkashin gwamnatin tarayya ta rufe
asusun ajiyarta ta koma yin amfani da
asusu daya tilo, wato TSA, wannan
mataki ya taimakawa gwamnati wajen
samun nasarar tattara kudaden da a baya suke dulmiyewa fiye da naira
tiriliyan 3. Asusun TSA ya kuma taimaka
wajen rage cin hanci, rashawa da
almundahana da dukiyar al’umma.
Sannan ya bawa Shugaban kasa damar
bibiyar yadda ake tafiyar da al’amuran kudade wajen shige da ficensu a
dukkanin hukumomin gwamnatin
tarayya. 7. Rage wadaka da kudi a gwamnati; kwarai da gaske zuwan Shugaba Buhari
ya sa gwamnati ta rage wadaka da
kudade ta hanyoyin da ba su da wasu
muhimmanci ga ‘yan Nijeriya. Buhari na zuwa ya sossoke duk wasu tafiye –
tafiye da ba za su taimaka wajen bunkasar Nijeriya ba, ya rage yawan
jami’an gwamnati da suke raka
Shugaban kasa a duk lokacin da zai yi
wata tafiya, sun rage yawan motocin da
suke binsa a baya. A baya – bayan nan
ya bada umarnin duk wani jami’in gwamnati da zai yi tafiya a hukumance
ya daina amafani da babbar kujerar jirgi,
sai dai ya yi amfani da kujerar ‘yan
kasuwa, irin wannan yunkuri ya
taimaka sosai wajen rage kudaden da
gwamnati ke kashewa a ba. A baya duk bakin da suka ziyarci fadar shugaban
kasa ta Aso Rock Billa, suna fitowa ne da
makudan kudi cike da aljihu, zuwan
Shugaba Buhari tuni hakan ya zama
tarihi. 8. Dawo da martabar Nijeriya a idanun duniya; Nijeriya na cikin kasashen da
suke da muhimmanci a duniya, Nijeriya
ce kasar da tafi kowace kasa yawan
jama’a a nahiyar Afrika, sannan a sahun
farko a duniya, mu muka fi kowace kasa
karfin tattalin arziki a Afrika, hasali ma duk wata kasa a nahiyar mu take kallo a
matsayin uwa, sai dai hakan ya faru ne
shekaru goma a baya, kafin zuwan
Shugaba Buhari, ba a nahiyar Afrika ba
ma, ko a yankin Afrika ta Yamma ba mu
da wani muhimmanci a idanun sauran kasashen, hatta makwabtanmu da mu
muke taimaka musu a koada yaushe
sun daina ganin girmanmu. Zuwan
Shugaba Buhari tuni hakan ya canja,
yanzu Nijeriya na komawa matsayinta,
Shugaba Buhari da zuwansa ya fara kai ziyara makwabtan Nijeriya ya zauna da
su an kuma daidaita zumunci, tun daga
lokacin suka koma ganin girman
Nijeriya duk wani abu da zai faru a
yankin Nijeriya kan gaba kamar yadda
yake a baya. A baya – bayan nan Nijeriya ta dauki nauyin taron zaman
lafiya na yankin yammacin Afrika
dukkan shugabannin kasashen sun
halarta, sannan Shugaban kasar Faransa
ya zama babban bako. 9. Cire tallafin man fetur; da dama za su yi mamakin ganin cire tallafin man fetur
a cikin nasarorin gwamnatin Shugaba
Buhari, sai dai wadanda suke bibiyar
yadda ake tafiyar da tallafin man na san
ba sa bukatar dogon bayani, kuma za su
gamsu lallai wannan babbar nasara ce da gwamnatin Buharin ta yi. Tallafin na
mai wasu ‘yan tsirarun mutane ne ke yin
rub da ciki a kansa, a yadda kididdiga ta
nuna kasa da kaso 1% na ‘yan Nijeriya
ke amfana da shi, shi kuwa Shugaba
Buhari ya zo ne domin talakawa, kuma ba zai taba barin duk wasu ‘yan
babakere su ci gaba da azabtar da
talakawan ba, na san zuwa yanzu an
fara fahimtar hikimar janye tallafin man,
kwarai da tallafin yana isa ga jama’a
Shugaba Buhari ba zai taba sanya hannu kan a cire shi ba. 10. Budaddiyar gwamnati; wato a tafiyar da gwamnati a bude yadda duk
dan kasa zai san hali da yadda ake
mulkarsa, irin haka ba a fiye ganinsa a
kasashen Afrika ba, tun zuwan Shugaba
Buhari babu wani mataki da gwamnati
take dauka a boye, duk matakan da take dauka, kusan wannan shi ne karo
na farko da gwamnati ta fitar da
cikakken kundin kasafin kudi domin
jama’a su gani sannan suke bibiyar
ayyukan da ke kunshe a cikin kasafin
kudin. 11. Nasarar dawo da kudaden Nijeriya da aka sace aka kai wasu kasashe, a
baya – bayan nan shirin dawo da dalar
Amurka milya 321 ya kammala wadda
kasar Switzerland ta yi alkawarin dawo
da su, Amurka da sauran kasashen da
kudaden Nijeriya ke can, an fara tattaunawa da su don ganin yadda za a
dawo da kudaden, wannan ya faru ne
sakamakon yarda da wadannan
kasashe suka yi da Nijeriya, Hadaddiyar
Daular Labarawa, wato UAE bayan dawo
da kudaden da ta yarda za ta yi, ta kuma sanya hannu da Nijeriya kan yarjejeniya
tsakanin kasashen ba wanda zai yadda
a sake shigo da wasu kudade cikin
kasarsu ba bisa ka’ida ba. 12. Cin hanci da rashawa; to fa, a wannan bangare na san ko masu
adawa da Gwamnatin Buhari za su ba ta
maki, tun zuwan Shugaba Buhari cin
hanci da rashawa a kasar nan a kullum
ja da baya yake yi, yanzu kowa na
tsoron hukumomin yaki da almundahana da dukiyar kasa, wato
EFCC da ICPC. Domin ya tabbatar da yaki
da cin hancin ya tafi yadda ya kamata,
Shugaba Buhari kafin ya cika kwanaki
100 a kan mulki ya bayyana
kadarorinsa, sannan ya umarci duk wani da ke cikin gwamnatinsa ya yi
hakan, zuwa yanzu kowa na ganin
yadda ake ta kaiwa da komowa a
kotunan kasar nan, hukuma ta garkame
mutanen da a baya sun fi karfin shari’a a
wannan kasa n. Bashir Ahmad, shi ne mai taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari kan
Sabbbin Kafafen Yada Labarai, ya rubuto
daga Abuja.

Admin
Admin

Posts : 3
Join date : 2016-06-05

View user profile http://wapharun.board-directory.net

Back to top Go down

Back to top


 
Permissions in this forum:
You cannot reply to topics in this forum